Ya hallaka ɗan uwansa, a zaton sa dabba ne

Ya hallaka ɗan uwansa, a zaton sa dabba ne

Wani lamari mai daure kai ya faru a kasar Amurka, can garin California inda wani mutum ya kashe dan uwansa.

Shi dai wannan mutum ya kashe dan uwan nasa mai suna Brian Pickle a lokacin da suke cikin farauta ranar 26 ga watan Nuwamba, sai dai yace ya dauka dabba ce ke wucewa

KU KARANTA: Zamu goge ma ýan fansho hawaye-Buhari

Jaridar Atalanta Journal ta shaida cewa Brian, kaninsa da mahaifinsu duk suna zaune ne a cikin wani daji, a can suke gudanar da rayuwansu. Shugaban yansandan yankin ya bayyana ma jaridar cewar lamarin ya faru ne gab da faduwar rana yayin da Scott Pickle ya kosa yayi farauta kafin dare yayi.

Dansandan yace, ana cikin haka nem sai Scott ya hango wani abu kamar Barewa zata wuce, nan da nan yayi seti ya harbota, ya ruga da gudu don dauko farautar sa, amma zuwansa ke da wuya sai yaga ashe dan uwansa ne Brian.

Dansandan yace “mun saba samun irin wadannan hatsarin” sai dai hukumar kula da gandun daji na California ta kasa tabbatar da laifin da zata tuhume shi da shi.

Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel