Wata mota tayi kisa, sakamakon tanka data fadi akan wat

Wata mota tayi kisa, sakamakon tanka data fadi akan wat

An bayyana cewar wata mota tayi kisa a jahar Abiya, sakamakon wata tankar mai mallakar kamfanin matatan mai wato NNPC data abka akan wata mota kirar marsandi.

Wata mota tayi kisa, sakamakon tanka data fadi akan wat

Tanka data fada akan mota kirar marsandi wanda ta janyo hasarar rayuka a garin Abiya.

Motar kamfanin matatar man dai tana dauke ne da man fetur na kimanin lita 40,000, wanda ta haye kan mota kirar marsandi daya janyo hasarar ran mai motar a daren ranar Asabar.

KU KARANTA: Kalli hoton hanya mafi hadari a Najeriya

Tankar dai mai dauke da nambar XKN 222 SA da kuma tambarin kamfanin matatar mai ta kasa wato NNPC, inda take kan hanyar ta na zuwa Oweri wato babban birnin jahar Imo, a inda motar ta kwacema direban ta a daidai kagan ginin makarantar kula da harkar kudade da sauran abubuwa makamantan su na sojin ruwa dake Owerrinta dake jahar Abiya.

Jaridar punch, ta rawaito cewar tankar ta dabi akan wata mota kirar marsandi mai ruwan bula inda ta nade direban.

A inda Caftin Abdullahi Aminu dake makarantar ta sojin ruwan, ya hada kan yaran sa inda sukai ta aikin watsa ruwa dan gudun kada wuta ta tashi a wajan.

Caftin Abdullahi Aminu ya kara dacewar, yana samu labarin faruwar mummunar hatsarin, sai yayi kokari ya hada kan yaran sa domin su taimaka dan ganin mutanen dake kusa da inda abin ya faru da subar wajen da sauri, dan gudun kada wuta ta tashi.

Inda yace " nayi kokarin gayama yarana cewar kada su kuskura subar mutanen dake kusa da wajan su zauna, domin tsaron rayukan su da kuma dukiyoyin su da kuma kare makarantar su daga fuskantar tashin gobara".

" Mutumin da tankar ta danne shi a cikin motar sa munyi kokarin daga tangar domin cetan lafiyar sa, amman wani abin ban tausayi shine, koda muka daga motar sai muka tarar ya mutu".

Asali: Legit.ng

Online view pixel