Rahma za ta yi sharia da Kannnywood

Rahma za ta yi sharia da Kannnywood

- Rahma Sadau ta ce tana da ja dangane da korar da kungiyar shirya finaifinan hausa ta yi mata

- Jarumar ta bayyana hakan ne shafinta na sada zumanta da muhawara na Facebook

- Kungiyar shirya fina-finan Hausa ta ce wannan ba shi ne karon farko da Rahma ta yi aikata irin wannan laifi ba

Rahma za ta yi sharia da Kannnywood
Rahama Sadau

Rahma Sadau fitacciyar Jarumar da kungiyar shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta haramtawa sake fitowa a cikin fina-finai, ta ce za ta garzaya kotu don kalubanlantar korar da aka yi mata.

Jarumar ta bayyana aniyarta na daukar wannan mataki ne a shafinta na sada zumunta da muhawara na Facebook, a inda ta lika wani takaitaccen sakon maratani ga korar ta na mai cewa, “Zan yi shari’a da Kannywood”, Sannan kuma ta a rubuta cikin harshen Ingilishi, "Shin Kannywood ce kadai inda ake shirin fim?"

A ranar lahadi 2 ga watan Oktoba ne kungiyar shirya finafinai ta Kannywood ta bayar da sanarwar sallamar jarumar daga finafinan hausa, bayan fitowarta a wani faifan bidiyo na waka tare da wani mawaki mai suna Classiq suna rungumar juna, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce.

Sai dai wasu bayanai na cewa, wannan ba shi ne karon farko da jarumar ta wuce gona da iri ba, kuma kungiyar na gargadinta amma ta yi kunnen kashi.

A hirarsu ba BBC, Shugaban Kungiyar, Muhammad Kabir Maikaba ya ce an dade ana muhawara kan irin hukuncin da ya kamata a dauka a kan 'yar wasan. Ya kuma da cewa da sau uku ke nan Rahama na aikata irin wannan danyen aiki, a inda a wannan karon har sai da aka yi kuri'a kuma masu son a kore ta suka yi rinjaye.

Malam Muhammad ya ce Rahama Sadau da sauran 'yan mata irinta suna matukar zubar wa kungiyar mutunci a idanun duniya. Haka ne ya sa kungiyar ta yanke shawarar korar 'yar fim din domin ta zamo izna ga masu ra'ayi irin nata.

Haka shi ma Sani Mu'azu tsohon shugaban kungiyar na kasa, a nasa shafin sada zumunta na Facebook ya yi bayanin yadda Rahma ya karya ka'idar kungiyar na yin badala a baya, ta kuma bayar da hakuri, har sa hannu a kan wani rubutaccen alkawari na ba za ta sake ba, amma sai ga shi ta sake aikata hakan, sai dai ya yi kira a gareta da ta tuba, ita kuma kungiya ta sassauta hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel