Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966

Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966

- An shiga rikicin siyasa bayan zaben  da akayi na 1964 yayin da NPC da NCNC da wani bangaren AG suka kafa gwamnatin gabin gambiza

- Wannan ya jawo rikice- rikice a jihar yamma inda aka rika kashe mutane ana kone-kone, abinda ya jaza kafa dokar ta baci a jihar

Haka dai akayi ta tafiya har safiyar 15 ga Janairu 1966 inda aka tashi da juyin mulkin da sojoji sukayi wanda yayi sanadiyar kisan prayim minista Abubakar Tafawa Balewa, firimiyan jihar arewa Ahmadu Bello, firimiyan jihar yamma Samuel Ládòkè Akíntọ́lá, ministan kudi Festus Okotie-Eboh da kuma wasu hafsan sojoji mafi yawansu daga arewacin kasar. Shin tun daga juyin mulki na farko har ya zuwa maido mulkin farar hula a shekarar 1979 ya zuwa maido da harkokin siyasa a 1999, wane ci gaba ko akasin haka 'yan siyasar Najeria da kuma shiyyar arewacin kasar suka samu?

Matsayin siyasa da 'yan siyasa kalkashin mulkin soja

Mutanen Arewacin Najeriya da 'yan siyasarsu sun yima juyin mulkin na farko kallon kokarin mutanen kudancin  Najeriya na amsar mulki ta bayan gida. Dokar gwamnatin sojojin ta farko itace dakatarda kundin tsarin mulkin kasar tare da korar 'yan majalisar tarayya dana jihohi, sannan aka nada gwamnonin soja ga jihohin

Major-General Johnson Aguiyi-Ironsi (16 Janairu 1966 - 29 Yuli 1966)

Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966

Wata shidda Ironsi yayi yana mulki kafin a hambaras da gwamnatinsa. Ba wani ci gaba da aka samu cikin lokacin, amma daga kamun ludayinsa na kirkiro dokar soja wadda ta hade kasar baki daya (unification decree) mamadin tsarin siyasar da aka sani mai ba jihohi 'yanci. 'yan arewacin kasar sunji tsoron mamayar harkokin kasar dama na yankinsu daga mutanen kudancin kasar

Janar Yakubu Gowon (1 Agusta 1966 29 Yuli 1975)

 

Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966

Bayan juyin mulkin daya hambarar da gwamnatin Ironsi, Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa, ya kuma yi mulki na kusan shekaru 10, a cikinsu harda shekaru biyu da rabi da akai ana yakin basasa (6 Yuli 1967 – 15 Janairu 1970).

Rashin sanin madafar mulki yasa Yakubu Gowon ya dauko 'yan siyasar da sojoji suka hambarar daga mulki domin taimaka masu wajen tafiyar da mulki kamar su:-

Chief Obafemi Awolowo - Ministan kudi kuma mataimakin shugaban majalisar zartaswa - yankin Yamma

Joseph Tarka - Ministan sufuri - yankin Arewa

Aminu Kano - Ministan sadarwa - yankin Arewa

Shehu Shagari - Ministan tattalin arziki- yankin Arewa

Anthony Enahoro - Ministan watsa labaru da kwadago - yankin Mid-west

An dama da 'yan siyasa lokacin mulkin Gowon, kuma an kirkiro jihohi 12 a kasar domin kwantar ma kananan kabilu hankali daga danniyar da suke jima tsoro daga manyan kabilu. Wannan babbar nasara ce a siyasar kasar. An kuma ci gajiyar arzikin mai da aka samu inda gwamnatin tayi manyan ayyukan raya kasa irin su hanyoyi, gine-gine da sauransu. Gowon yayi alkawarin mika mulki ga farar hula, alkawarin daga baya ya saba

Janar Murtala Muhammed (30 Yuli 1975 13 Febrairu 1976)

Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966
General Murtala Muhammed

Lokacin mulkin Murtala Muhammad, an hana harkokin siyasa kamar kowane mulkin soja, amma yasa ranar mika mulki ga farar hula. Fiye da rabin ministocinsa farar hula ne. Ya hukunta jami'an gwamnati da aka samu da almundahana. Ya kuma karfafa matsayin Najeriya a siyasar Afrika dama ta duniya yayin daya bada goyon bayan Najeriya ga kungiyar MPLA ta Angola. Mulkinsa bai yi tsawon da za'a iya auna fai'dar dake cikin sa ba ko akasin haka. An kashe shi a yunkurin juyin mulki da soja sukayi ranar 13 ga Febrairu 1976

Janar Olusegun Obasanjo (13 Febrairu 1976 30 Satumba 1979)

Siyasa da 'Yan Siyasar Najeriya tun Juyin Mulkin 1966

An samu arziki lokacin mulkin Obasanjo wanda akayi amfani dashi wajen ayyukan gina kasa irinsu birnin tarayya Abuja. Matatun mai, madatsun ruwa domin noman rani da cibiyoyin wutar lantarki wanda bangarorin kasar suka amfana

Gwamnatin Obasanjo tayi kokari gyaran mulkin kananan hukumomi, kuma ta cika alkawarinta yayin da ta gudanar da zabukka ta kuma mika mulki ga farar hula a 1979.

Mulkin sojoji daga 1983 zuwa 1999

Rashin iya mulki, da rashin hadin kan 'yan siyasa tare da cin hanci  da rashawa yasa aka hambarar da mulkin

Shehu Shagari a 1983. Kafin a sake maido da mulki wajen farar hula anyi mulkin sojoji na janar Muhammadu Buhari, janar Ibrahim Babangida, janar Abacha da janar Abdussalami Abubakar kafin karnin da muke ciki na mulkin 'yan siyasa tun 1999

Daga karshe

Har ya zuwa zaben 2015, za'a iya cewa siyasar kasarmu da 'yan siyasar basu kaucema magudin siyasa, cin hanci da rashawa ba, tare da siyasar addini data bangaranci.

Idan mutum zai amfani da ma'aunin abubuwa irin su gina kasa kamar su raya ilmi, masana'antu, aikin gona, zaman lafiya da sauransu, za'a iya cewa anfi samun ci gaba lokacin mulkin soja fiye dana farar hula. Amma wani tsohon dan siyasa mai basira (Chief Obafemi Awolowo) yace wanda gara mulkin farar hula mafi lalacewa da kyakkayawan mulkin soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel